Connect with us

Labarai

Jami’an tsaro sun kashe yan bindiga 12 tare  kwato dabbobi da makamai a wurinsu

Published

on

Jami’an tsaro, sun kashe ‘yan bindiga 12 tare  kwato dabbobin da aka sace da kuma makamai a dazukan da ke tsakanin kananan hukumomin Kurfi da Safana na jihar Katsina.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Dakta Nasiru Mua’zu, ne ya bayyana hakan ta cikin  wata sanarwa da ya fitar a daren jiya Laraba, inda ya ce, an kaddamar da farmakin ne a matsayin martani ga harin da bata garin suka kai da sanyin safiyar ranar Laraba  a kauyen Rahamawa da ke gundumar Kuraye a karamar hukumar Charanchi.

Mua’zu ya ce, maharan sun afka wa al’ummar ne da misalin karfe 5:40 na safe, inda suka raunata wani magidanci Alhaji Danmalam mai shekaru 60, tare da yin awon gaba da shanu 22.

Sai dai bayan samun rahotannin sirri cikin gaggawa, rundunar hadin gwiwa da ta kunshi jami’an yan sanda da Sojoji da jami’an kula da jama’a na jihar, da ’yan banga na yankin suka bi sawun barayin bayan da suka tsere zuwa Dutsen Falale da ke yankin Kurfi zuwa Safana inda aka yi musayar wuta da ya yi sanadin mutuwar ‘yan bindigar 12.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!