Labarai
Jami’an tsaro sun kashe yan ta’adda 592 a Borno

Gwamnatin Nariya ta ce jami’an tsaro sun samu nasarar kashe yan ta’adda 592 a jihar Borno daga watan Maris zuwa Nuwamban bana.
Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a zantawar sa da manema labarai.
Ya ce a watan Maris, wani rahoto da Cibiyar Global Terrorism Index, mai tattara bayanai kan ta’addanci ta nuna cewa hare-haren ‘yan ta’adda sun ragu sosai a kasar a wannan lokaci.
Ya kuma kara da cewa gwamnati za ta kara daukar matakan domin tabbatar da tsaro a fadin Najeriya
You must be logged in to post a comment Login