Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shalkwatar tsaro ta tabbatar da kashe manyan ‘yan ta’adda

Published

on

Shelkwatar tsaro ta ƙasa ta tabbatar da kashe wasu fitattun kwamandojin ‘yan ta’adda hudu a hare-haren da aka kai ta sama cikin mako guda.

Ƴan ta’addan su ne Machika, Haro, Dan Muhammadu da Ali Alhaji Alheri, wanda aka fi sani da Kachalla Ali Kawaje.

Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Maj.-Gen. Edward Buba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar a Abuja.

Buba ya ce Machika babban kwararre ne mai haɗa bama-bamai ne kuma kanin fitaccen dan ta’adda (Dogo Gide) ne, yayin da Haro da Dan Muhammadu suka kware wajen yin garkuwa da mutane.

Ya ce wani farmakin hadin gwiwa da sojojin sama da na kasa suka kai a ranar 11 ga watan Disamba ne yai sanadiyar kashe Kachalla Kawaje, wani fitaccen shugaban ‘yan ta’addan da ke da alhakin sace daliban Jami’ar Tarayya ta Gusau, Zamfara.

Ya kara da cewa an kashe Kachalla ne a karamar hukumar Munya ta Nijar tare da wasu yaran sa da dama.

A cewarsa, sojoji sun kisa cimma sauran ƴan ta’addan, yayin da wasu kuma za su fuskanci irin wannan halin nan gaba kadan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!