Labarai
Jami’an tsaro na hadin gwiwa 5000 ke yaki da ta’addanci a Arewa maso gabashin Najeriya – Sufeto
Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar nan Usman Baba Alkali, ya ce, jami’an ‘yan sanda da sojoji akalla dubu biyar ne ke aikin yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso gabashin kasar nan.
Usman Baba Alkali ya yi wannan jawabi ne jiya Litinin 5 ga watan Yuli a shelkwatar ‘yan sanda da ke birnin tarayya Abuja, lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar matan jami’an tsaro ta kasa karkashin jagorancin shugabarta Mrs Victoria Irabor.
Babban sufeton ‘yan sandan, ya ce, ‘yan sanda da sojoji suna aikin hadin gwiwa don magance matsalolin tsaro a arewacin kasar nan da ma Najeriya baki-daya, har ma da aikin wanzar da zaman lafiya a kasashen waje.
A na ta jawabin Mrs Vctoria Irabor, ta ce sun ziyarci babban sufeton ‘yan sandan ne domin karfafawa jami’an tsaron kasar gwiwa wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
You must be logged in to post a comment Login