ilimi
Jami’ar Dutsen jihar Jigawa za ta fara koyar da harkokin shari’a da injiniya
Jami’ar tarayya da ke Dutsen jihar Jigawa ta shirya tsaf don koyar da fannin harkokin shari’a da Injiniya kari kan wadanda ta ke da su.
Jami’ar ta ce tana aiki don samar da cibiya guda daya wacce za ta kula da bincike kan dukkan bangarorin karatun dalibai a jami’ar tare da bangarori daban-daban kamar su sashin tarbiyya da bangaren bada shawara kan harkokin kudi.
Sai kuma bangaren da zai rika saurarar koken dalibai da kuma samun gurbin karatu da sauran korafe-korafe.s
Shugaban jami’ar, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed ne ya bayyana hakan a jiya Laraba a wani taron tattaunawa da ‘yan jarida don bayyana wasu muhimman ayyukan da za su kara bunkasa makarantar.
You must be logged in to post a comment Login