Labaran Kano
Jam’iyar APC ta kammala gabatar da shedunta kan zabe gwamna na jihar Kano
Jam’iyyar APC da gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, sun kammala gabatar da shaidun su gaban kotun sauraran korafin zaben gwamnan jihar ta Kano a yau Juma’a.
Yayin zaman kotun na yau dai, lauyoyin gwamman na Kano sun gabatar da daraktan yakin neman zaben gwamna Ganduje, Alhaji Nasiru Aliko Koki, a matsayin shaidar su ta karshe.
Sai dai lauyan jam’iyyar PDP da dan takararta Abba Kabir Yusuf, Barista Eyitayo Fatogun, ya tambayi Alhaji Nasiru Aliko Koki da cewa, ko yaushe ya fara siyasa, wanda ya ba da amsa cewa, ‘ya fara siyasa tun a alif da dari tara da saba’in da takwas’.
Haka zalika Barista Eyitayo Fatogun, ya kuma tambayi Nasiru Aliko Koki cewa, ‘ko ya sa ido kan zaben gwamna da ya gudana’? Inda ya kada baki ya bayyana cewa, a matsayinsa na daraktan yakin neman zaben gwamna, wajibi ne gareshi ya sa ido kan zaben.
A cewar sa, ya sa ido a zaben da aka gudanar a ranar tara ga watan Maris, sai dai ya ce, an kada kuri’a da suka wuce adadin kuri’un da aka tantance da kuma hatsaniya, lamarin da ya yi sanadiyar soke zaben musamman a mazabar Gama da yankin karamar hukumar Dala.
A jiya alhamis ne dai, jam’iyyar ta APC da dan takararta Dr. Abdullahi Umar Ganduje suka gabatar da shaidu uku.