Labarai
Jam’iyyar ADC ta sanya 14 ga Afrilu domin babban taron ta na kasa

Jam’iyyar adawa ta ADC ta sanar da cewa za ta gudanar da babban taronta na kasa a ranar 14 ga Afrilu, 2026, domin zaben sabbin shugabannin jam’iyyar na kasa.
A cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar, ya ce an tsara jerin tarukan zaben shugabanni daga matakan kasa da kasa na jam’iyyar domin sabunta shugabanci kamar yadda kundin tsarin jam’iyyar ya tanada.
Sanarwar ta ce za a fara da tarukan zaben shugabanni a rumfunan zabe da unguwanni ranar 7 ga Afrilu, sai na kananan hukumomi a ranar 9 ga Afrilu, sannan na jihohi a ranar 11 ga Afrilu, kafin a kammala da babban taron kasa a ranar 14 ga Afrilu.
Jam’iyyar ta ce wannan tsari na daga cikin kokarinta na karfafa dimokuradiyya a cikin jam’iyyar, tare da shirye-shiryen tunkarar zaben shekarar 2027.
You must be logged in to post a comment Login