Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jam’iyyar APC a Kano ta shigar da ƙara gaban kotun ƙorafin zaɓe

Published

on

Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta shigar da ƙara gaban kotun ƙorafe-ƙorafen zaɓe, inda take ƙalubalantar nasarar Abba Kabir Yusuf, a matsayin gwamnan Kano a zaɓen 18 ga watan Maris ɗin bana.

Cikin ɓangarorin da jam’iyyar mai mulki ke ƙara a gaban kotun, har da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), da ɗan takarar da aka ayyana a matsayin wanda ya ci zaɓen gwamnan Kano, da kuma jam’iyyarsa ta NNPP.

APC dai ta ce Abba Gida-Gida, bai ci zaɓen gwamnan Kano da halastattun ƙuri’u ba.

Mashawarcin APC ta Kano kan harkokin shari’a, Barista Abdullahi Adamu Fagge, kuma ɗaya daga cikin lauyoyin da ke wakiltar jam’iyyar, ya shaida wa kafar BBC cewa, sun nemi kotu ta ayyana ɗan takarar jam’iyyarsu na APC, a matsayin wanda yake da rinjayen halastattun ƙuri’u.

Sai dai ko da na tuntubi Lauyan NNPP na Kano Barista Barshir Yusuf Tudun Wuzurci, ya ce ‘duk da cewa babu wanda ya kai ga basu sammaci, amma tabbas tsagin masu ‘kara basuma fahimci me doka tace ba’.

Rahoton: Abdulkadir Haladu Kiyawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!