Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Jigawa

Son zuciya ne yasa aka samar da Inconculusive – Garba Ɗantiye

Published

on

Tsohon dan  Majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Garki da Ɓabura a jihar Jigawa  Nasiru Garba Ɗantiye, yace  son zuciya ne ya sa aka samar da  tsarin Inconclusive a kasar nan.

Nasir Garba Ɗantiye ya bayyana hakan ne a zantawar sa da Freedom Radio.Ya ce duk Ƙasar da ta samu cigaba to harkokin  zaben Ƙasar ana gudanar da shi cikin gaskiya da adalci,

“a baya munga yadda aka gudanar da wani sabon  tsarin mai suna Inconclusive, wanda a doka  bamu san shiba ƙirƙirsa kawai a kai,”

duk zaɓen da akai aka bayyana shi a matsayin Inconclusive to zakaga son   zuciya  na biyu baya domin babu shi kuma bamu san shi a doka ba,”

“A ƙasar nan muna da hukumar zabe  mai zaman kanta INEC, sai dai duk gwamnatin da ke shugabancin wannan lokacin to fa itace ke gudanar da ita,

shiyasa muke cewa ba za’a taba samun zabe mai inganci ba muddin hukumar bata samu damar ikwan gudanarwa da kanta ba,”

“Muna ganin yadda a wasu guraren ake samun wasu da suke kada kuri’u ciki harda kananan yara,  kuma kowa ya san da hakan gwamnatoci da hukamar zaɓe  suna gani amma babu wani mataki da suke iya ɗauka ,”

“A irin haka ne fa ake  gudanar da wani abu wai shi Inconclusive  wanda jami’iyyar da ba  sune ke da mulki ba idan sun ci zabe sai a ki fada hakan ne yasa ake samun zaɓen mara inganci ,”

“Lokacin tsohon shugaban hukumar Farfesa Attahiru Jega ne aka samar da wata na’ura da zata rika tantance masu zaɓe, da shugaba Muhammad Buhari da ‘yan majalisu duka sun  samu nasara a lokacin

Tsohon ɗan majalisar Nasir  Garba Ɗantiye ya  ce idan har anaso ‘yan Ƙasa su gamsu da irin zaɓen da ake gudanarwa to kawai a kirga kuri’u a inda aka gudanar da zaben.

Haka zalika ya ce sabuwar hanyar gudunar da zabe ta hanyar kafar Sada zumunta zata tsaftace yadda zabuka a ƙasar nan zasu inganta.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!