Labarai
Jam’iyyar APC ta fitar da jadawalin taron ta na 25 ga watan Maris a shekarar 2026

Jam’iyyar APC ta fitar da jadawalin taron ta na kasa wanda zai gudana daga ranar 25 ga watan maris zuwa 28 ga watan na shekarar 2026.
Bayanin haka na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na Kasa Senator Ajibola Basiru, ya fitar a shafin sa na X.
A cewar sanarwar da jam’iyyar ta fitar, ta ce wannan jadawali zai bai wa mambobinta damar yin shiri yadda ya kamata domin gudanar da zabuka cikin tsari da kwanciyar hankali a dukkan matakai, kafin babban taron kasa.
APC ta jaddada cewa wannan mataki na daga cikin kokarin jam’iyyar na karfafa dimokiraɗiyya a cikinta, da tabbatar da shugabanci nagari da haɗin kai a faɗin kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login