Labarai
Jam’iyyar APC ta zabi sabon shugabanta na kasa

Jam’iyyar APC, ta zabi Farfesa Nentawe Yilwatda dan asalin jihar Filato mai shekaru 56, a matsayin sabon shugabanta na kasa.
Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodima, ne ya gabatar da kudirin nada sabon shugaban wanda shi ne minista jin kai inda shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen ya mara masa baya.
An zabe shi ne a yau Alhamis a taron maalisar Koli na jam’iyyar APC wanda ke gudana a Abuja, inda kuma aka rantsar da shi nan take.
Ya karbi mulki daga hannun Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya sauka daga mukaminsa a kwanan baya saboda rashin lafiya.
A halin yanzu Farfesa Yilwatda, shi ne ministan harkokin jin kai kuma ya taba zama malamin jami’a.
Ya fito ne daga jihar Filato kuma shi ne dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben 2023.
Zaben nasa ya biyo bayan wata yarjejeniya da aka cimma a wata ganawar dare da aka yi a Abuja tsakanin shugaba Bola Tinubu da gwamnonin APC.
You must be logged in to post a comment Login