Labarai
Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta yi watsi da taron da uwar jam’iyyar ta yi a Abuja

Tsagin jam’iyyar NNPP a nan Kano yayi watsi da taron da jam’iyyar ta gudanar a Birnin tarayya Abuja, wanda ta bayyana shi a matsayin haramtacce.
Shugaban tsagin jam’iyyar, Sanata Mas’ud El- Jibril Doguwa ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Jaridar Punch a yau Lahadi.
Sanata Doguwa yace taron da aka gudanar, taro ne na kungiyar Kwankwaso kawai, don haka ya sabawa ka’ida.
El- Jibril Doguwa ya bayyana banagaren da yake shugabanci za su cigaba zama masu bin doka da Oda.
You must be logged in to post a comment Login