Siyasa
Jam’iyyar PRP ce za ta iya dawo da martabar siyasar Najeriya – Abba Sule Namatazu
Jam’iyyar PRP a Najeriya ta ce, yadda ake gudanar da shugabanci a Najeriya da jihohin ta ya sa za ta dawo a zaben shekarar 2023 domin tsaftace siyasar kasar.
Shugaban jam’iyyar a jihar Kano Alhaji Abba Sule Namatazu, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da Jam’iyyar ta gabatar a ranar 12 ga watan Maris na shekarar 2022.
Ya kuma ce “Muna fatan kara farfado da jam’iyyar domin sake gabatar da ita a jihohin Arewa maso yammacin Najeriya da suka hadar da jihar Kano da Jigawa da Zamfara da Sokoto da katsina da Kebbi da kuma jihar Kaduna”.
Alhaji Abba Sule Namatazu ya ce “A yanzu haka kasar nan na fama da matsaloli da suka hadar da tabarbarewar Ilimi da Tattalin Arziki da Tsaro wanda hakan yake da bukatar a sake dawo da siyasa irin ta su marigayi malam Aminu Kano ta kishin kasa”.
Da yake Jawabi yayin taron mai magana da yawun jam’iyyar ta PRP a jihar Kano Alhaji Musa Mai Gari ya ce “fatan mu shine kafa gwamnati a jihar Kano dama sauran jihohin kasar nan duba da cewa jam’iyyar ta zagaya ko ina a Najeriya”.
Ya kuma ce a shirye suke wajen yin tafiya da kowa a cikin jam’iyyar domin tabbatar da an ciyar da Najeriya gaba.
You must be logged in to post a comment Login