Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Makarantu su cusawa ɗalibai ɗabi’ar shuka bishiya – Dakta Getso

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci makarantu da su mayar da hankali wajen cusawa ɗaliban su ɗabi’ar shuka bishiya.

Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan lokacin da yake ƙaddamar da dasa bishiyoyi a titin zuwa sabuwar jami’ar Bayero.

Getso ya ce “Da ace shugabannin makarantu za su mayar da hankali wajen sanya ɗalibai su shuka bishiya a gida ko a makarantu, to kuwa jihar Kano za ta fita daga yanayin da take ciki”.

Za mu fara aikin gyaran titin Gayawa a ƙaramar hukumar Nasarawa – Ganduje

“Yanzu haka gwamnati ta mayar da hankali wajen dasa bishiyoyin da za su zamo dukiya anan gaba, don bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa, amma ƙudurin gwamnatin na inganta muhalli da ƙawata shi, ba zai cika ba har sai al’umma sun bayar da gudunmawar da ta dace, musamman kulawa da abubuwan da ake samarwa.” a cewar Getso.

Kwamishinan muhallin ya bayyana hakan lokacin da yake ƙaddamar da dasa bishiyoyi tun daga ƙofar Kabuga zuwa sabuwar jami’ar Bayero.

Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da aka kammala rukuni na farko na makon dashen bishiya a jihar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!