Labarai
Jigawa: Ƴan sanda sun cafke mutanen da ake zargi da satar Dabbobi

Rundunar ’yan sandan jihar Jigawa ta ce, ta samu nasara wajen kama wasu da ake zargi da satar shanu da tumaki, tare da kwato dabbobi da kayayyaki da aka sace a sassa daban-daban na jihar.
Mai magana da yawun rundunar, SP Shisu Lawan Adam, ya ce an samu nasarar ne sakamakon jajircewar kwamishinan ’yan sanda na jihar, Dahiru Muhammad, da kuma hadin gwiwar mutanen jihar.
Daga cikin wadanda aka kama akwai Usman Yusuf, wanda aka samu da saniyar da aka sace a Malam Madori, Isubu Adamu da Danladi Maikudi da aka kama a Hadejia da shanu biyu a cikin mota ba tare da rajista ba, sannan kuma Umaru Audu da aka cafke da shanu biyu da aka sace a Kaugama.
Haka kuma, jami’an sun kama wani Ali Alh. Buji da ake zargi da hannu a satar shanu da tumaki goma sha uku a Taura, sai kuma Amadu Muhammad da aka kama da wayoyin wutar lantarki da aka lalata a Guri LGA.
Kwamishinan ’yan sanda ya yaba wa jami’an rundunar da masu sa-kai bisa kwazo, tare da tabbatar da cewa za a ci gaba da kai farmaki a maboyar masu laifi domin tabbatar da tsaro.
You must be logged in to post a comment Login