Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Jigawa

‘Yan Sanda a Jigawa sun kama wasu matasa da satar shanu

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta samu nasarar kama wasu mutane hudu wadanda take zarginsu da laifin satar Shanu da kuma wasu Wayoyin Hannu.

Mai magana da yawun rundunar ASP Abubakar Isah ne ya bayyana hakan ga manema labarai da yammacin jiya Alhamis.

ASP Abubakar Isah ya kara da ‘cewa wadanda ake zargin su hudu sun sato Shanun ne guda shida a wani gida, kuma an kama sune a jihar Bauchi akan hanyarsu ta zuwa siyarda Dabbobin da suka sato’.

Freedom Radio ta rawaito cewa ‘rundunar na cewa da zarar ta kammala gudanar da bincike akan wadanda ake zargin za’a gurfanar dasu a gaban Kotu.

Rahoton: Abdulkadir Muhammad Abdulkarim

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!