Jigawa
Jigawa: NUJ ta sha alwashin yin aiki tare da hukumar PCACC

Kungiyar ‘yan Jarida ta Najeriya reshen jihar Jigawa, ta jaddada alakar yin aiki tare da hukumar karbar korafi da yaki da cin hanci don tabbatar tsantseni tsakanin ma’aikatun da hukumomin gwamnatin jihar.
Da ya ke jawabi a yayin ziyarar da kungiyar ta kai ofishin shugaban Hukumar Barista Salisu Abdu, shugaban kungiyar ta NUJ Kwamared Isma’il Ibrahim Dutse, ya ce, kafafan yada labarai na taka rawa a ayyukan hukumar wajen wayar da kan mutane sanin damar da suke da ita ta shigar da korafi ko rahoton wata almundahana.
Da ya ke mayar da jawabi shugaban hukumar Barista Salisu Abdu ya ce, aikin hukumar na da alaka da na ‘yan Jarida ta wajen wayar da kan mutane sanin illar cin hanci da yin aiki bisa ka’ida ba.
Haka kuma, ya ce hukumar na da ikon gayyato wadan da aka shigar da korafi a kan sa tare da gudanar da bincike bisa tsarin doka, ya yin da ‘yan Jarida kuma ke da ikon fayyace gaskiyar lamari ta hanyar rubutu ko magana.
Ya kuma bai wa kungiyar tabbacin yin aiki tare da kuma samar da tsarin da hukumar za take fitar da bayanai lokaci zuwa lokaci ga al’umma game da aiyukan ta.
You must be logged in to post a comment Login