Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Jigawa

Jigawa : Wani barawon Babura ya shiga hannu

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wani matashi daya kware wajen satar babura, a daidai lokacin da yake shan jibga a hanun wasu mutane.

Kafin hakan dai rundunar tace ta karbi rahoton sace wani babur Roba-Roba  da ake kirar  da Lifan a unguwar Yelwawa Dutse, bayan bincike suka gano matashin ne barawon da ya saci baburin.

Matashi mai suna Muhd Yahaya Auwal dan asalin jihar Kano mai shekaru 22, ya amsa da bakin sa cewa shine ya saci babur din dama wasu da dama.

Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa SP Abdu Jinjiri yace matashin ya shaidawa jami’an hukumar su cewa, yana amfani da mukullai daban-daban wajen satar Baburan mutane.

Yanzu haka dai rundunar tace suna cigaba da bincike kan matashin inda da zarar sun kammala za su gurfanar da shi gaban kotu.

Wakilinmu Muhd Aminu Umar Shuwajo ya rawaito cewa, ana yawan samun korafin satar babura a masallatai da ma’aikatu da sauran gurare a jihar ta Jigawa.

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!