Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Ministoci da gwamnoni ku dinga girmama umarnin ‘yan majalisa – Buhari

Published

on

Shugaban kasa muhammadu Buhari ya gargadi minstocin kasar nan da gwamnoni dasu rika girmama umarnin da majalisun dokokin kasar nan da suke bayar a kowani matakai.

Hakan na cikin wata sanarwar da ma shawarcin shugaban kasa kan harkokin yada labarai mallam Garba Shehu ya fitar.

A cewar sanarwar shugaban kasa muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da shugabanin majalisun biyu a jiya Alhamis.

Yayin ganawar,shugaba Buhari da shugaban Majalisar dattijai Ahmad Lawan da takwaransa na wakilai Femi Gbajabiamila sun koka kan yanda wasu daga cikin ministocin kasar nan basa biyayya ga umarinin Majalisar.

Ganawar  tsakanin shugabanin  da aka shafe tsawon awani ana gudanarwa ana tattauna mahimman abubuwa da suka shafi kasa da suka  hadar da harkokin tsaro, kamar yanda sanarwar ta bayyana.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!