Labarai
Jigawa: Yan sanda sun cafke mutane 13 da ake zargi da aikata manyan laifuka

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da kama mutane 13 ciki har da mutane biyar da hukumar ta ke nema ruwa a jallo, bisa zargin su damfrar jama’a ta hanyar canjin kudaden ketare.
Rundunar, ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mataimakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ASP Ibrahim Idris, ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce, bayan korafe-korafe kan wadanda ake zargi kan laifin damfara fashi da makami da kuma sauran munanan laifuka, ya sanya rundunar yan sandan ta hada hannu da jami’an soji, da kuma yan sandan farin kaya na DSS, gami da jami’an Civil defence
Daga cikin wadanda aka kama sun hada da Salisu Ibrahim, da Umar Dauda, Abdullahi Umar, sai kuam Magaji A. Mohd da kuma Abubakar Ibrahim.
Yayin sumamen dai, hukumomin sun samu nasarar kama takardun kudade da suka hada da Naira, da kuma dalar Amurka baya ga wayoyin hannu sama da guda biyar, sai katin sahaidar zama dan kasa.
You must be logged in to post a comment Login