Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar ‘yan sandan Bauchi ta kama mutane 7 da ake zargin ‘yan fashi ne

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wasu mutane 7 da ake zargin ‘yan fashi ne a maboyar su dake unguwar Magaji.

Rundunar ‘yan sandan ta ce, wadanda ake zargin ba su wuce tsakanin shekaru 17 zuwa 25 ba, kuma an same su da makamai masu hatsari da kuma barasa’.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchin Ahmed Mohammed Wakil ya fitar, tace ‘wadanda ake zargin sun hadar da Rayyanu Mohammed, Mustapha Harisu, Yusuf Ibrahim, Mubarak Lawal, Abubakar Musa, Al-Amin Hussaini da kuma Hamza Umar’.

Kamen dai ya biyo bayan bayanan sirri da rundunar tace ta samu tare da hadin guiwa da jami’an sa kai.

A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ‘binciken farko ya nuna wanda ake zargin ‘yan wata kungiya ne mai suna Sara Suka dake gudanar da ayyukan su a cikin kwaryar birnin Bauchi’.

Rahoton: Abdulkadir Yusuf Gwarzo

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!