Labarai
Jigawa: Yan sanda sun kama matasa 3 bisa zargin su da safarar kwayoyi

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, ta kama wasu matasa uku da ta ke zargi da safarar miyagun kwayoyi a fadin jihar.
Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ya fitar SP Shisu Lawan Adam, ya fitar yau Talata a birnin Dutse.
SP Shisu Lawan, ya kuma ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar 18 ga watan Oktoban nan da muke ciki a Garki da Fagam da Maigatari, inda suka kama miyagun kwayoyin da adadin su ya kai 23,944 wadanda ake zargin dai daya ya fito daga Jihar Kano yayin da dayan kuma ya fito daga jamhuriyar Nijar.
Rundunar ta kuma bayyana cewa, yanzu haka matasan da ake zargin su na sashen binciken laifukan miyagun kwayoyi domin ci gaba da bincike.
You must be logged in to post a comment Login