Labarai
Jigawa:kotu ta yankewa wani mataimakin darakta a hukumar INEC hukunci daurin shekara shida
Wata babbar kotun jihar Jigawa ta yanke hukuncin daurin shekaru shida ga wani mataimakin darakta a Hukumar zabe ta kasa INEC Auwal Jibrin sakamakon zargin sa da arzuta kansa ta hanyar karbar nagoro.
Alkalin kotun mai shari’a Yusuf birnin kudu, ya kuma yanke hukuncin shekaru bakwai ga wani mutum mai suna Garba Isma’ila, sakamakon amfana da yayi da kudaden da tsohuwar ministar man fetur Diezani Allison Madueke ta raba gabanin zaben shekarar dubu biyu da goma sha biyar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai rikon mukamin jami’in yada labaran Hukumar EFCC Mista Tony Orilade.
Sanarwar ta ce alkalin kotun ya yanke hukuncin ne a ranar juma’a da ta gabata sakamakon gurfanar da su da Hukumar ta EFCC ta yi gaban kotun.
Sanarwar ta kara da cewa, mutanen biyu sun karbi cin hanci naira miliyan arba’in da biyar cikin naira miliyan dari biyu da hamsin da tsohuwar ministar Diezani Allison Madueke ta turo jihar Jigawa gabanin zaben shekarar dubu biyu da goma sha biyar.