Manyan Labarai
Jihar Kano ce kan gaba wajen gurbatar muhalli- Airvisual
Rahoton wata kungiya mai zaman kanta mai suna IQ Airvisual ,dake zaman ta a kasar Switzeland ta ayyana jihar Kano a matsayin jiha da ta fi kowacce jihar fuskantar gurbatar muhalli a fadin nahiyar Afrika, wanda mafi yawan gurbatar ke ta’allaka da gurbacewar iska da kimanin fiye da kaso 54 na iskar da ake shaka.
Rahoton ya bayyana cewa abinda ke haddasa yawan gurbacewar iskar sakamakon yawaitar ma’aikatun da ke fitar da hayaki , wasu lokutan kumab dagwalon masana’antu da kone itatuwa domin samar da gawayi na daga cikin abinda ke haifar da gurbacewar muhallin.
Binciken dai ya bayyana cewar birnin Kampala na kasar Uganda ce ta biyu bayan jihar Kano.
Sai Fatakwal dake jihar Rivers wanda ta zo ta uku, sannan Addis Ababa dake kasar Habasha wacce it ace ta zo ta hudu a duk fadin nahiyar Afrika.
Jaridar Kano Focus ta rawaito cewar Kano ce ke kan gaba a jeren jihohin da ke fuskatantar gurbatar muhalli a fadin Duniya, da kimanin kaso 44 cikin dari, sannan kasar Uganda da Habasha.
Kungiyar ta IQ Airvisual ,ta ce nahiyar Afrika na fama da matsalolin gurbatar muhalli sakamakon rashin samun wayar da kai yadda ya kamata wajen inganta nahiyar Afrika.
Menene gurbatar muhallin iska
Gurbatar muhallin iska wani abu ne da ayyukan dan Adam na yau da kullum ke haifar da shi, wanda yake da illa ga iska da muke shaka , baya ga kawo cikas da yake yi ga muhalli da muke ciki na yau da kullum.
Bincike ya nuna cewar akalla kimanin mutane fiye da miliyan 3 ne ke mutuwa sakamakon gurbatar muhalli ,musammam ta hanyar iska a duk shekara , walau ta hanyar amfani da itatuwa ko gawayi ko kalanzir da dai sauransu.