Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jihohin da suke ikirarin kirkiro da ‘yan sandan jihohi basa iya albashi – Buhari

Published

on

Fadar shugaban kasa ta ce da yawa daga cikin jihohin da ke ikirarin neman basu damar kirkiro da ‘yan sandan jihohi ba sa ma iya biyan albashi na ma’aikatan da su ke da shi a wannan lokaci.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Garba Shehu ne ya bayyana haka yayin zantawa da gidan talabijin na Channels.

Malam Garba Shehu ya ce ya kan yi mamaki idan yaji jihohin da ma’aikatansu ke binsu tarin albashi na watanni masu yawa amma suna korafin cewa sai an basu dama sun samar da ‘yan sanda.

Y ace gwamnatin tarayya tana iya kokarimnta wajen ganin ta dakile ayyukan batagari a kowane sassa na kasar nan.

Malam Garba Shehu ya kuma ce wannan dalili ne ya sanya gwamnati ta ke kokarin ganin an samar da ‘yan sandan al’umma wanda zai taimaka gaya wajen magance matsalolin tsaro.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!