Labarai
Jirgin Kasan da ya tashi daga Kaduna zuwa Abuja ya yi hatsari

Rahotonni daga jihar Kaduna na cewa wani jirgin kasa da ke kan hanyar zuwa Abuja ya yi hadari a safiyar Litinin.
Sai dai, rahotonni sun bayyana cewa, ba a samu asarar rayuka ba, sai dai jikkatar da mutane da dama su ka yi.
A cewar wasu da hadarin jirgin kasan ya ritsa da su, an sanya karin Ttarago ne lokacin da jirgin ya isa Jere, lamarin da ya haddasa hatsarin.
Bayanai sun ce, an dauki tsawon lokaci gabanin gyara jirgin tare da ci gaba da tafiya zuwa birnin tarayya Abuja.
A cewar shaidun gani da ido, dimbin fasinjan jirgin sun galabaita yayin da suke a firgice saboda fargabar abin da ka je ya zo.
You must be logged in to post a comment Login