Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jirgin Saman Kamfanin Dana Ya Tsallake Rijiya Da Baya: DANA AIR

Published

on

Mahukuntan kamfanin jiragen sama na Dana Air sun tabbatar da rahoton cewa, daya daga cikin jirginsa ya tsallake rijiya da baya a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas a safiyar yau Talata.

Kamfanin jirgin ya tabbatar da hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a yau Talata 23 ga watan Afrilun 2024.

Kamfanin ya kuma ce jirgin da ya taso daga Abuja zuwa Legas, ya kauce daga titin jirgin a kokarinsa na sauka ne.

Sai dai sanarwar ta bayyana jin dadin ta da cewa ba a samu asarar rai ba, inda ta bayyana cewa ta sanar da hukumar binciken haddura da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa lamarin don faɗaɗa bincike.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!