Labarai
Jirgin Sojin Najeriya ya yi mummunan hadari

Wani jirgin sama marar matuki na rundunar sojin saman kasar nan ya fadi a dajin Zangata, da ke karamar hukumar Kontagora a Jihar Neja.
Rahotanni sun bayyana cewa jirgin saman na cikin wani aikin sa ido ne a yankin lokacin da lamarin ya faru, sai dai har zuwa lokacin fitar da wannan rahoto, rundunar sojin sama ba ta bayyana ainihin dalilin da ya sa jirgin ya faɗi ba.
Majiyoyi sun ce babu rahoton asarar rai, kuma an rufe yankin da lamarin ya faru domin gudanar da bincike kan musabbabin faduwar jirgin.
You must be logged in to post a comment Login