Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

Jirgin mu yayi mummunan hatsari a Kaduna – Sojin sama

Published

on

Rundunar sojin saman ƙasar nan ta tabbatar da cewa jirginta yayi hatsari.

A cikin sanarwar da mai magana da yawun rundunar Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar, ta shafin Twitter ya ce, hatsarin ya faru ne da yammacin yau Jumu’a a kusa da garin Kaduna.

Sanarwar ta ce, yanzu haka ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin faruwar haɗarin.

Sai dai sanarwar ba ta yi ƙarin bayani kan waɗanda lamarin ya rutsa da su ba.

Amma tuni manyan jaridun ƙasar suka rawaito cewa, hatsarin ya rutsa da Babban Hafsan Sojin saman ƙasar da mataimakansa, wanda kuma yayi ajalinsu nan take.

A wani saƙon Twitter da ya wallafa mai taimakawa shugaban ƙasa na musamman kan tallafawa mabuƙata Barista Isma’il Ahmad ya yi ta’aziyya bisa rasuwar Babban Hafsan Sojin, wanda hakan ke gasgata labarin rasuwar ta su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!