Connect with us

Labarai

Jiri ne ya ɗebe ne a lokacin da na ke jawabi a fadar shugaban ƙasa – Abdurrashid Bawa

Published

on

Shugaban hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa EFCC Abdurrashid Bawa ya ce, likitoci sun tabbatar da cewa ya samu ƙarancin ruwa a jikin sa, a daidai lokacin da yake jawabi a fadar shugaban ƙasa.

Abdurrashid Bawa ya bayyana hakan lokacin da ake hira da shi a gidan talabijin na Channels awanni kaɗan bayan farfaɗowar sa.

Bawa ya ce ‘lokacin da lamarin zai faru Na fara jin jiri, sai kuma Na yanke jiki Na faɗi, lamarin da ya janyo hanakalin jama’ar gurin suka ba ni ɗaukin gaggawa”.

Idan za a iya tunawa da safiyar ranar Alhamis ne shugaban EFCC ɗin ya yanke jiki ya faɗi a fadar shugaban ƙasa, daidai lokacin da yake bayani a wani ɓangare na bikin ranar katin ɗan ƙasa.

Abdurrashed Bawa ya kuma ce, ya samu lafiya tun bayan da ya samu kulawa daga wajen likitoci, har ma ya koma bakin aiki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!