Connect with us

Labarai

JOHESU da sauran jami’an lafiya za su yi Zanga-zanga a fadin Najeriya

Published

on

Ƙungiyoyin ma’aikatan lafiya ƙarƙashin inuwar JOHESU da sauran Ƙungiyoyin da ke aikin Lafiya sun sanar da shirinsu na gudanar da zanga-zanga a fadin Najeriya musamman ma a birnin tarayya Abuja, kan wasu sabbin dokokin harkar lafiya na shekarar 2026 da ke gaban Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

 

Ma’aikatan lafiyar dai sun shirya gudanar da zanga-zangar ne a yau Alhamis, 26 ga watan Maris, inda ake sa ran ma’aikatan lafiya daga sassa daban-daban na ƙasar za su hallara a harabar Majalisar Dokoki, bayan sun taru a Unity Fountain da ke Maitama a Abuja.

 

A wata sanarwa da aka fitar da safiyar yau, ƙungiyar JOHESU ta umarci dukkan ƙungiyoyinta da su tattara mambobinsu domin halartar zanga-zangar, tana mai gargadin cewa sabbin dokokin na iya yin tasiri mai yawa ga ma’aikatan lafiya da kuma tsarin kiwon lafiya gaba ɗaya.

 

Sakataren ƙungiyar na ƙasa, Martin Egbanubi, wanda ya sanya hannu kan sanarwar, ya ce zanga-zangar na da matuƙar muhimmanci domin wayar da kan Rahotanni sun nuna cewa dokokin, waɗanda tuni suka tsallake karatu na farko a Majalisar Dattawa, sun janyo damuwa a tsakanin ma’aikatan lafiya, saboda yiwuwar sauya tsarin aiki, rawar da kowane ɓangare ke takawa, da kuma jin daɗin ma’aikata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!