Labaran Wasanni
Jonathan ya bude sabon filin wasanni a Yenagoa
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kaddamar da sabon wajen gudanar da wasanni mai suna GEJ Sports Club don samar da matasan ‘yan wasa masu hazaka a Najeriya.
Jonathan ya kuma nemi hadin gwiwar masu ruwa da tsaki a harkokin wasanni yayin taron kaddamarwar a garin Yenagoa dake jihar Bayelsa.
Ya ce, samun hadin gwiwa daga masu ruwa da tsaki da abin ya shafa zai taimaka wajen kula da kuma bunkasa hazikan matasa da za a yi gogayya da su a fagen wasanni a fadin duniya.
Ya kuma yaba wa wadanda suka halarci taron, kamar yadda ya bayyana cewa GEJ Club House za ci gaba da karɓar bakuncin wasannin cikin gida daban-daban.
You must be logged in to post a comment Login