Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

NPFL: Rivers United ta gabatar da korafi kan Jigawa Golden Stars

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Rivers United ta shigar da korafi ga kamfanin shirya gasar League ta kasa LMC ta na kalubalantar Jigawa Golden Stars da yin amfani da dan wasan da aka dakatar daga buga wasanni.

Jigawa Golden Stars dai ta yi amfani da dan wasa Christopher Richard da aka dakatar sakamakon samun katin gargadi masu yawa a gasar cin kofin kwararru ta kasa da ake gudanarwa.

Hakan ya faru ne a fafatawar da kungiyar tayi da Rivers United a ranar wasa ta 34 da aka yi a jihar Kaduna.

A cewar ka’idojin LMC na gasar, “Idan har aka tabbatar da cewa, da gangan wata kungiya tayi amfani da dan wasan da aka bawa katin gargadi biyar (5) ko jan kati kafin wasan da ake magana, kungiyar da abin ya shafa za ta rasa maki uku da ci uku ga abokiyar hamaiyarta.”

Kwamishinan wasanni na jihar Rivers, Boma Iyaye ya yi kira ga LMC da ya yi adalci a kan karar don ci gaba da karfafa wa kungiyoyin da masu gudanarwa da kuma magoya baya gwiwa a gasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!