Labaran Wasanni
Juventus ta karrama Ronaldo da riga mai lamba 770

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Juventus Andrea Agnelli ya bai wa Cristiana Ronaldo sabuwar riga ta musamman.
Rigar dai na dauke da lambar iya kwallayen da Ronaldo ya ci tun a lokacin da ya fara taka wasa zuwa yanzu tare da taken “Fitatcen Gwarzon Dan Wasan Kowane Lokaci.”
Kawo yanzu dai Ronaldo na da kwallaye 770 a tarihin wasannin da ya buga, lamarin da ya sanya kungiyarsa ta Juventus ta bashi kyautar sabuwar rigar.
Ronaldo ya yi nasarar zama gwarzon dan wasan gasar Serie A na wannan shekarar a ranar Juma’a da ta gabata 19 ga watan Maris, wanda shine karo na biyu a jere.
You must be logged in to post a comment Login