Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Wa zai lashe kyautar gwarzon dan wasan nahiyar Turai?

Published

on

Kevin De Bruyne da Robert Lewandowski da kuma Manuel Neuer na cikin jerin sunayen ‘yan wasan ukun farko da za a baiwa kyautar gwarzon dan wasa a gasar UEFA ta shekarar 2019/2020.

A baya-bayan nan ne dai De Bruyne wanda ya ke taka leda a Manchester City ya lashe kyautar gwarzon dan wasan shekara a Firimya ta kasar Ingila. A yayin da Robert Lewandowski da Manuel Neuer da suke a kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich sun tallafa wa bangaran su wajen karewa a mataki na uku a kakar wasa da ta gabata.

Haka kuma, dan wasan bayan Liverpool Virgil van Dijk ya samu irin wannan karramawar a kakar wasa data wuce, inda ya baiwa Lionel Messi da Cristiano Ronaldo rata.

Kawo yanzu dai UEFA ba ta bayyana matakin kowane daya daga cikin ‘yan wasa guda uku, yayin da kuma ta fadi wanda ya zo mataki na hudu zuwa na goma.

Haka zalika, ‘yan wasan Barcelona Lionel Messi da Neymar ne suke a mataki na hudu, yayin da dan wasan Juventus Ronaldo ya sauka zuwa mataki na 10.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!