Labaran Wasanni
Manchester United ta cimma yarjejeniyar da Juventus na daukan Cristiano Ronaldo
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta cimma yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Juventues dake kasar Italiya, wajen kara daukan tsohon dan wasan ta Cristiano Ronaldo.
Manchester United dai ta amince da biyan Yuro miliyon 12.8 kan daukan Ronaldo daga kungiyar ta Juventus.
Ronaldo mai shekaru 36 kafin barin sa kungiyar ta Manchester United zuwa Real Madrid dake kasar Spaniya a shekarar 2009, ya zurawa kungiyar kwallaye 118 cikin wasanni 292 da ya buga mata.
Manchester City ta cimma yarjejeniya da Juventus kan Ronaldo
A wata sanarwa da kungiyar ta Manchester United ta fitar yau Juma’a 27 ga Agustan 2021, ta ce masoyan kungiyar na murnar sake dawowar dan wasan nata Cristiano Ronaldo.
A jiya Alhamis 26 ga watan Agusta abokiyar burmin Manchester United wato Manchester City ta bayyan cewar za ta dauki Cristiano Ronaldo, kafin daga bisani Manchester United ta shiga cikin cinikin.
You must be logged in to post a comment Login