Labarai
Ka cire tallafin man fetur kawai – majalisar kula da tattalin arzikin kasa ga Buhari
Majalisar koli ta kasa da ke ba da shawara kan harkokin tattalin arziki, ta shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ba da umarnin cire tallafin man fetur kwata-kwata ba tare da bata lokaci ba.
A cewar majalisar da ke da hurumin bai wa shugaban kasa shawara kan al’amuran tattalin arzikin Najeriya, ta ce, hakan ne kawai zai kasar nan za ta samu sassauci daga mawuyacin halin da ta ke ciki na karanci kudi a wannan lokaci.
A shekarar 2019 ne shugaba Buhari ya kafa majalisar kolin karkashin jagorancin farfesa Doyin Salami don maye gurbin tsohon kwamitin kula da tattalin arziki na kasa wanda mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ke jagoranta.
Haka zalika majalisar ta ce ci gaba da biyan tallafin man fetur a wannan lokaci yayin da a bangare guda gwamnati ba ta sanya tallafin cikin kasafin kudin da ta yi ba, ba abin da hakan zai haifar sai kara dagula al’amura, saboda a yanzu nauyin biyan tallafin man fetur din ya rataya ne akan kamfanin mai na kasa NNPC.
You must be logged in to post a comment Login