Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

Kaduna: An sake gano gawarwakin wasu ɗaliban jami’ar Greenfield

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce, masu garkuwa da mutane sun kashe ƙarin ɗalibai biyu cikin ɗaliban jami’ar Greenfield da suka sace.

Hakan na cikin wata sanarwa da Kwamishinan al’amuran tsaro da addini na jihar ya fitar da yammacin ranar Litinin.

Sanarwar ta ce, Gwamnatin jihar ta karɓi rahoton daga jami’an tsaro na sake gano gawarwakin ɗaliban guda biyu.

Gwamnan jihar Malam Nasir El-rufa’i ya bayyana takaicin sa kan wannan kisan gilla da aka yiwa ɗaliban da ba su ji ba basu gani ba.

Gwamnan ya miƙa saƙon ta’aziyyar sa ga iyalai da ƴan uwan waɗanda lamarin ya shafa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!