Labarai
Kaduna: MHWUN ta musanta cewa ta na shirin tsunduma yajin aiki

Kungiyar Ma’aikatan Lafiya ta kasa MHWUN, reshen Jihar Kaduna, ta musanta jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa tana shirin shiga yajin aiki a fadin jihar.
A cewar wata sanarwa da aka aika wa Shugaban Ma’aikata na jihar, ƙungiyar ta ce ba ta da wata niyya ko shiri na yajin aiki a Kaduna.
Kungiyar ta yabawa gwamnatin Jihar bisa matakan da ta dauka wajen inganta bangaren lafiya.
Kazalika ta yaba mata bisa yadda ta sabunta Asibitoci 255, da kuma samar da muhimman kayayyakin aiki ga cibiyoyin lafiya a jihar.
You must be logged in to post a comment Login