Labarai
Kaduna: Yan sanda sun musanta rahoton yin garkuwa da mutane 160 a coci-coci

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta musanta rahotannin da ake yaɗawa na garkuwa da sama da mutane 160 a wasu coci-coci da ke ƙauyen Kurmin Wali a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
Rundunar ta ce wasu marasa kishi ne ke yaɗa wannan labari da nufin tayar da hankalin jama’a.
A jiya Litinin ne wasu daga cikin jaridun kasar nan suka bayar da rahoton sace mutane fiye da 100 a wuraren ibadah daban-daban na ƙauyen Kurmin Wali, inda suka ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 18 ga watan Janairu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban ƙungiyar kiristocin kasar nan CAN, reshen jihar Kaduna Reberan Joseph John ya tabbatar mata da aukuwar lamarin.
You must be logged in to post a comment Login