Kiwon Lafiya
Kaduna:kotu ta dage karar jagorar mabiya darikar shi’a
Babbar Kotun tarayya dake zama a jihar Kaduna ta dage zaman sauraran karar jagoran mabiya darikar sha’a Ibrahim El-zakzaky da mai dakin sa Zeenat.
A cewar Kotun ta dage cigaba da suraran karar ne biyo bayan nada alkalin dake jagorantar shariar mai shari’a Gideon Kudafa a matsayin manba a kotun sauraran kararrakin zabe dake jihar Yobe.
Tun da fari dai babbar kotun ta tarayya ta sanya yau 25 ga watan da muke ciki na Maris don cigaba da sauraran zarge-zaegen karar da ake yi wa jagoran darikar Shi’a.
Shi dai jagoran mabiya darikar Shi’a Ibrahim El-zakzaky da mai dakin sa Zeenat ana zargin su da aikata kisan kai da hada gangamin taro da ya sabawa ha’ida, da kuma kawo tashin hankali da dai sauran su.
Haka zalika a yayin zaman kotun na karshe a ranar 22 ga watan Janairu bara wanda mai shari’a Gideon Kurada ke jagoranta ya hana bai wa wadanda ake zargi bele.
A cikin takardun karar da lauyan Ibrahim El-zakzaky Femi Falana ya shigar gaban kotun, ya nemi kotun ta bada umarnin da a fitar da wanda ake kara da mai dakin sa zuwa kasashen ketare don duba lafiyar su.
Har ila yau a cikin kunshin takardun lauyan ya bukaci gwamnati ta baiwa wanda ake zargin damar kawo likitoci daga kasashen waje don duba lafiyar sa kafin sake zaman kotun na yau. Sai dai alkalin kotun ya bada umarnin jagoran mabiya darikar shi’a da mai dakin sa, su cigaba da zama a hannun hukumar tsaro ta farin kaya DSS har lokacin da za’a kammala shari’ar da ake yi musu