Connect with us

Kiwon Lafiya

Jigawa:Gobara ta kone gidaje da dama a kauyen Barebari

Published

on

Gobara ta kone gidaje da dama  a kauyen Barebari dake karamar hukumar Ringim a jihar Jigawa.

Babban sakatare a hukumar bada agajin gaggawa na jihar Alhaji Sani Yusuf ne ya tabbatar da tashin gobara a birnin Dutse.

Gobarar wacce ta tashi da misalin karfe 11 na safiyar jiya Talata har zuwa yammacin  karfe 6 kafin a shawo kan ta, ta yi sandiyar lalata gidaje da dama.

Alhaji Sani Yusuf ya ce kawo yanzu ba’a sanar da musababin tashin gobarar ba.

Rahotanni sun bayyana cewar, gobarar dai ta cinye dukkanin ilahirin gidajen yankin na Bare-Bari dake karamar hukumar Ringim tare da dabbobi da kayayyakin abinci.

Babbban sakataren a hukumar bada agajin gaggawa na jihar ya ce gidajen yankin da suka kone za su iya kai wa guda 60 bayan da wuta ta cinye su kurmus.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,889 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!