Labarai
Kafa Masaku zai bunkasa tattalin arzikin kasa -MD
Kamfanin Mudassir and brothers da ke nan Kano, ya ce zai samar da wata masaka a wani yunkuri na samarwa matasan jihar Kano aikin yi.
Shugaban kamfanin Alhaji Mudassir Idris Abubakar ne ya bayyana hakan yau, jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan tashar Freedom Radiyo, wanda ya yi duba kan inganta masana’atun cikin gida da suka jima da durkushewa.
Alhaji mudassir Idris ya kuma ce, rufe iyakokin kasar nan ya kawo cigaba matuka ta fuskar bukansa tattalin arzikin kasa.
Batutuwa masu nasaba
kamfanoni 30 ne suka aike da bukatar karbar jinginar ma’aikatar albarkatun ruwa
Tsohon gwamnan bankin CBN ya ce kamata yayi a samar da asusun tallafawa kananan masana’antu
A na sa bangaren, shugaban masakar Adhama textile, Alhaji Sa’idu Dattijo Adhama, ya ce, kafa kamfanonin masaku a jihar nan na da alfanu sosai musamman na Auduga wanda ya ke da matukar amfani.
Bakin dai sun yi kira ga gwamnati tarayya da na jihohi da su tallafa musu wajen kawo ci gaban masana’antu a fadin kasar nan, don fadada komar tattalin azikin kasar da kuma samar da aikin yi ga al’umma.