Connect with us

Labarai

Hukumar EFCC ta mikawa jami’ar Dutsinma motocin sata

Published

on

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC , reshen jihar Kaduna ta mika motoci guda hudu da ta kwato  daga hannun wasu hukumomin jami’ar tarayya ta Dutsinma dake jihar Katsina ga hukumomin jamia’ar.

Mai magana da yawun hukumar  Mr Wilson Uwujaren ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja , ya ce an samo motocin ne biyo bayan takarda da ministan ilimi Malam Adamu Adamu ya fitar.

Mr Uwujaren yace ministan yana zargin wasu daga cikin shugabannin jamia’ar da biyan kansu wasu miliyoyin kudade a matsayin alawus , tare da sanya kansu wasu ayyukan da ake zarginsu da cin hancin da rashawa ta hanyar amfani da bankin First bank.

Wasu daga cikin laifukan da ake zarginsu da shi sun hadar da almundahana wajen sayo kayayyakin aiki da kara kudadensu ta hanyar kara farashi, da kuma baiwa wasu kwangiloli ta hanyar hadin baki da kara kudade.

Hukumar EFCC ta cafke masu kamfanin boge da bindigu a Kano

Kayayyakin da aka kwato sun hadar da wasu motoci Toyota corolla guda biyu mai dauke da lamba FUDMA 51F -03FG da FUDMA 51F-05FG, sai wata Toyota Land Cruiser ZTRJ150L mai dauke da lamba FG 668 – E45 da kuma Toyata Camry XLE 205 da kuma ABC 601 LX.

Da yake mika kayayyakin, shugaban hukumar EFCC reshen jihr Kaduna Mailafia Yakubu  ya ce an saki motocin ne biyo bayan bukatar jami’ar na sakar motocin.

Ya ce mika musu motocin na daga cikin irin ayyukan da hukumar

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,337 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!