Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kai tsaye: An dai cigaba da tantance kwamishinoni

Published

on

Kai tsaye: An dai cigaba da tantance kwamishinoni

A halin da ake cikin shugaban majalisar dokoki ya kira Muhammad Sunusi Kiru yayin da fara bayanai kan rauywar sa.

Muhammad Sunusi Kiru dai yayi aiki a ma’aikatar Wasanni ta kasa.

Kuma dan majalisa Sale Ahmed Marke daga mazabar Dawakin Tofa ke masa tamabayoyi.

Kunshin sunayen da gwamnan ya aikewa majalisar dokoki sun hada da:

Engr. Muazu Magaji

Barrister Ibrahim Muktar

Musa Iliyasu Kwankwaso

Dr. Kabiru Ibrahim Getso

Mohammed Garba

Nura Mohammed Dakadai

Shehu Na’Allah kura

Dr. Mohammed Tahir

Dr. Zahara’u Umar

Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa

Sadiq Aminu Wali

Mohammed Bappa Takai

Kabiru Ado Lakwaya

Dr. Mariya Mahmoud Bunkure

Ibrahim Ahmed Karaye

Muktar Ishaq Yakasai

Mahmoud Muhammad

Muhammad Sunusi Saidu

Barrister Lawan Abdullahi Musa

A halin yanzu dai ana tsaka da tantance Ibrahim Ahamed Karaye yayin da aka fara tambayar sa da cea ko ya taba rike mukamin kwamishina.

Wakilin mu Abdullahi Isa ya rawaito cewa, akasarin tambayoyin da ake wadanda ake tantancewar bai wuce ko sun rike mukamai ba da kuma yadda suke gudanar da ayyukan su ba.

Shugaban majalisar Abdu’aziz Garba Gafasa na dai tantancewar ne da harshen turanci yayin da kuma wasu ‘yan majalisar ke yi musu tambayoyi da harshen Hausa.

Bayan da majalisar ta zauna da misalin karfe goma, shugaban majalisar Abdul’azizi Garba Gafasa ya fara kiran sunayen da gwmanan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya aike musu.

An dai fara da Musa Iliyasu Kwankwaso sai Muhammad Garba da Murtala Sule Garo da kuma Dr, Mariya Muhamoud Bunkure

Harabar majalisar dokoki ta jihar Kano ta dauki harabi biyo bayan sunayen da gwamnatin Kano ta aikewa majalisar a jiya.

Da safiyar yau Talata ne wakilin mu na majalisar dokoki ta jihar Kano Abdullahi Isa ya rawaito cewar an dauke matakan tsaro a ciki da wajen harabar majalisar.

Wakilin na mu ya kara da cewar wadanda aka aike da sunayen na su tuni wasu suka isa harabar majalisar yayin da kuma wasu  ke shiga  cikin majalisar a halin yanzu.

Kai tsaye: An dage cigaba da zaman majalisar Kano

Kai tsaye: Har yanzu ba’a kama Zakin da ya kubuce ba

Kai tsaye: Yadda shari’ar zaben Gwamnan Kano ke gudana

Ana sa ran nan gaba kadan ne majalisar dokoki ta jihar Kano zata fara zaman tantance kunshin sunayen da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya aikewa majalisar a jiya litinin.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!