Connect with us

Labarai

Kalaman Ɓatanci: PDP ta nemi Ali Baba ya bai wa Kwankwaso haƙuri

Published

on

Jam’iyyar PDP mai adawa a Kano ta bai wa mai bai wa gwamnan Kano shawara kan al’amuran addinai Ali Baba A Gama Lafiya Fagge wa’adin awanni 48 kan ya nemi afuwar tsohon gwamna Injiniya Rabi’u Kwankwaso.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na Kano Bashir Sanata ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio.

Sanata ya ce, suna neman Ali Baban ya nemi afuwar Kwankwason kan kalaman da ya yi na ɓatanci a kan sa na zargin shi ne ya mallaki gidajen man Aliko Oil.

A ranar Lahadi ne dai ƴan sanda suka bada belin Ali Baba Fagge, bayan da ya janye kalaman da ya yi na jingina gidan man Alikon da tsohon gwamna Kwankwaso.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,433 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!