Labaran Kano
Kamata ya yi kungiyoyi su dinga taimakawa gidajen marayu- Aisha Dangi
Shugabar kungiyar Sustainable Dynamism Hajiya Aisha Dangi ta ja hankalin kungiyoyi dasu rika taimakawa gidajen marayu da kayan more rayuwa.
Hajiya Aisha Dangi ta bayyana haka ne lokaci da take ziyara gidan marayu dake asibitin Nassarawa a nan kano.
Ta kara da cewa kamata ya yi gwamnatin jihar kano ta samar da wajen da za’a koyawa marayu sana’oin da zasu dogara da kansu.
Haka kuma Hajiya Aisha dangi tace sun kawo musu kayan abinci kayan sawa, katifa bargo da dai sauransu.
A nata jawabin shugabar gidan na marayu Hajiya Lauriya Sagir tace suna yabawa kungiyoyi domin suna kokari wajen taimakawa marayu da kananan yara da suka rasa iyaye.
Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa marayun suna kira da Gwamnati data samar musu wajen da zasu rika koyan sana’oin da zasu dogara da kansu ba sai sunje gurin mutane suna rokinsu su taimaka musu da wata