Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

Kamata yayi gwamnatin tarayya ta ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta’adda – El-rufa’i

Published

on

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta’adda da ke barazana ga zaman lafiyar Arewa maso gabashin ƙasar nan.

Nasir El-Rufai ya bukaci hakan lokacin da ya ke karɓar rahoto kan al’amuran tsaro daga hannun kwamishin harkokin tsron jihar Samuel Aruwan.

Ya ce ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta’adda zai bai wa jami’an tsaron Najeriya damar murkushe ƴan bindigar ba tare da fargabar cewa ƙasashen duniya za su sanya musu takunkumi ba.

“Mu a gwamnatin jihar Kaduna a koyaushe muna yin kira da a ayyana ƴan ta’adda a matsayin masu tayar da ƙayar baya, domin kuwa mun rubuta wasiƙa zuwa ga gwamnatin tarayya tun daga shekarar 2017 muna neman wannan buƙata”.

Nasir El-Rufai ya kuma ce suna goyon bayan ƙudurin da majalisar dokoki ta kasa kan ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta’adda.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!