Labarai
Kamfanin NNPC sun fara safarar man fetur kasashen Burkina Faso da Mali da Cote d’Ivore
Kamfanin mai na kasa (NNPC), ya ce, masu fasakwaurin man fetur a kasar nan suna safarar sa zuwa kasashen Burkina faso da Mali da kuma Cote d’Ivoire.
A cewar kamfanin na (NNPC), ‘yan fasakwaurin suna kuma safarar man fetur din zuwa kasar Ghana domin sayar da shi su ci riba.
Babban jami’in gudanarwar kamfanin na NNPC Henry Ikem-Obih ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Abuja.
Ya ce, yayin da ake sayar da farashin Litar man fetur akan naira dari da arba’in da biyar a kasar nan a sauran kasashen da ke makwabtaka da kasar nan, ana sayarwa akan naira dari uku da hamsin da kuma dari hudu da talatin.