Kiwon Lafiya
Kamfanin NNPC ya karbi kudin tallafin Mai kusan Tiriliyan 5 daga 2006 zuwa 2015
Kamfanin Mai na kasa NNPC ya shaidawa majalisar Dattijai cewa ya karbi kudi kusan Naira Tiriliyan 5 a matsayin kudin tallafin Mai daga shekarar 2006 zuwa shekarar 2015.
Babban Jami’in kudi na NNPC Malam Isiaka Abdulrazak ne ya sanar da hakan a jiya Litinin lokacin taron jin ra’ayin jama’a da majlisar ta shirya a Abuja dangane da al’amuran da suka shafi man fetur din.
Shugaban kamfanin Man Maikanti Baru ne ya jagoranci manyan jami’an kamfanin a yayin taron, bayan da Majalisar ta yi sammacinsu dangane da halin matsalar karancin Man da ake ci gaba da fama da shi a kasar nan.
Malam Isiaka Abdulrazak ya shaidawa majalisar cewa biyan kudin tallafin ya samu sahalewar hukumar kayyade farashin man fetur ta kasa.
Sai dai duk da wannan kudi da aka biya har yanzu matsalar karancin man fetur din ta ki ci ta ki cinyewa a kasar nan, inda ake ci gaba da fuskanra dogayen layukan sayen man a gidajen man a fadin kasa baki-daya.
Sai dai majalisar Dattijan ta umarci kamfanin na NNPC ya kawo karshen matsalar nan da makon farko na watan Fabarairu mai kamawa.